
Alfijr ta rawaito Ma’aikatar tsare-tsare da raya birane ta jihar Lagos ta tabbatar da rugujewar wani bene mai hawa bakwai wanda ba a amince da shi ba, a tsibirin Banana da ke yankin Ikoyi na jihar.
Wata majiya daga hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyanawa gidan talabijin na Channels cewa wasu ma’aikata sun makale a cikin baraguzan ginin.
An kuma tattaro cewa lamarin ya faru ne a kan titin First Avenue da ke unguwar kebabbun wasu attajiran Najeriya.
Kadan da suka samu raunuka ana jinya.
Binkenan da aka fitar na farko babu mutuwa ya zuwa yanzu, wadanda suka samu raunuka kuma suna can ana cigaba da kulawa da su.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da ake yin wasan kwaikwayo,” in ji mataimakin daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar, Mukaila Sanusi.
kwamishinan tsare-tsare da raya birane, Engr. Tayo Bamgbose Martins, ya ziyarci wurin “nan da nan” don tantance halin da ake ciki tare da kaddamar da bincike.

“Muna rokon jama’a da su kwantar da hankalinsu kuma su yi tsammanin karin bayani daga ma’aikatar kamar yadda muka sani,” in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ