
Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yansandan Jihar Filato ta tabbatar da cafke wasu ‘yan sanda biyar da ake zargi da harbe wani dan kasuwa mai suna Ibuchim Ofezie har lahira a kasuwar Terminus da ke unguwar Jos a jihar.
Wani ganau ya bayyana cewa wanda aka kashe ya samu rauni ne sakamakon harbin bindiga da daya daga cikin ‘yan sandan ya yi,
Wani dan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan sandan na kan babura uku ne, sai daya daga cikinsu ya bude wuta har harsashin ya same shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce an kama ‘yan sandan da suka yi kuskuren.
Ya ce, “Don tabbatar da cewa tawagar sintiri da ta yi kuskure ba ta kauce wa shari’a ba, kwamishinan yan sanda jihar ya bayar da umarnin kama jami’an.
An kama jami’an biyar da suka hada da ‘yan sintiri, kuma a halin yanzu ana binciken su a sashen binciken kisan gilla na hukumar binciken manyan laifuka ta Jihar Jos.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ