
Alfijr ta rawaito Gwamna Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 138 a gidan gwamnatin jihar.
Gwamnan Kanon ya jagoranci aikin ne a daren daren jiya Lahadi.
A jawabinsa bayan musuluntar da mutanen maza da mata da suka fito daga karamar hukumar Sumaila, gwamna Ganduje ya ja hankalinsu game da kulawa da Ibada tare da neman Ilimin addinin Musulinci.
Yayi kiran ga wadanda suka musulunta da su yi kokari wajen bin dokokin Allah SWT, da yin riko da koyarwar addini.
Wasu daga cikin wadanda suka karbi muslinci sun bayyana cewa wa’azin da sukeji a unguwanninsu a cikin Azumi ya taka muhimmiyar rawa wajen jan hankalinsu domin su shiga addinin.
Wasu daga cikin su sun ce suna samun nutsuwa da addinin wanda hakan yasa suka amince su shiga domin su cigaba da gudanar da rayuwarsu akan tafarkin gaskiya da kuma tsari.
A yayin taron, an raba kayan Sallah ga wadanda suka musulunta maza da mata tare da raba musu jari domin su dogara da kansu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ