Daga Aminu bala madobi.

Alfijr ta rawaito rahotanni sun nuna cewa an shiga ‘yar wasan buya tsakanin jami’an Rarara da Jami’an kotu ke binshi dan bashi sammacin tuhumar kudi sama da Milyan Goma.
An gurfanar da shahararren mawakin ne a gaban kotun shari’ar addinin musulunci dake zaman ta a Rijiyar Zaki karkashin Mai shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariya.

Tunda fari wani mai suna Muhammad Ma’aji ya maka Dauda RARARA a gaban kotun kan kwashe masa kudade Naira Milyan 10 da suka kulla wata harka a watanni da suka gabata.
Mai karar ya shaidawa kotun cewa bashi da wani zabi face ya gurfanar dashi gaban kuliya domin kwato masa hakkin sa.
Mai karar Muhammad Ma’aji yace yabi dukkan hanyoyi nayin sulhu amma abin yaci tura.
Karin bayani na nan tafe….
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ